Connect with us

News

‎Mace Ɗaya Ta Mutu, Shida Sun Jikkata Yayin Da Bus Ta Yi Karo Da Tipa 

Published

on

lagos car crash
Spread the love

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta tabbatar da mutuwar wata mace ɗaya, sannan wasu mutane shida sun ji rauni a wani hatsarin mota da ya afku a Majidun, kan hanyar Ikorodu.

‎Hatsarin ya faru ne lokacin da motar Bus mai ɗauke da fasinjoji ta buge babbar motar tipa da ke tsaye a gefen hanya.

Ruftawar Mahakar Ma’adanai Ta Yi Ajalin Sama Da Mutum 100

‎A cewar Daraktan Yaɗa Labarai na LASTMA, Adebayo Taofiq, binciken farko ya nuna cewa motar Bus ɗin, wacce aka ɗauka haya zuwa wani taro a Ogijo, ta samu matsalar birki yayin da direban ke tuƙi da sauri, lamarin da ya haifar da hatsarin.

‎Sakamakon hatsarin, wata mata ta rasu nan take, yayin da mata biyar da namiji ɗaya suka jikkata. An garzaya da su Asibitin Benic Special domin kulawa da lafiyarsu.

Advertisement

‎LASTMA ta ce jami’anta sun kama direban tipar wanda ya yi ƙoƙarin tserewa, tare da direban Bus ɗin, sannan an mika su ga rundunar ‘yan sandan Ipakodo domin ƙarin bincike.

SAHARA REPORTER

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *