News
Mun Kammala Fiye Da Kashi 80 Na Alkawuran Da Aka Yi a Lokacin Yakin Neman Zaɓe — Gwamnan Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kammala sama da kashi 80 cikin 100 na alkawuran da ta dauka a lokacin Yakin neman Zaɓe, a Cikin shekaru biyu da rabi kacal ke nan da fara mulki.
Gwamnan ya sanar da haka ne a ranar Laraba, yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2026, wanda ya kai N1,368,127,929,271.00, ga Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Gwamna Yusuf Ya Ɗauki Masu Gadi 1,600 Aiki Don Kula Da Tsaron Makarantu A Kano
A cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an ce wannan ci gaba na nuna “tsantsar jajircewa da mayar da hankali wajen aiwatar da alkawuran da suka shafi rayuwar jama’a.”
“Muna farin cikin cewa fiye da kashi 80 cikin 100 na shirye-shiryenmu sun riga sun kammalu, suna shafar fannoni da dama, tare da kawo tasiri kai tsaye a rayuwar al’umma,” in ji Gwamnan.
Ya ce gabatar da kasafin kudin na wannan shekara ya zo ne a wani lokaci mai muhimmanci, inda ake bukatar hanzari da tsantsar aiwatarwa domin cikar alkawuran da aka yi wa mutanen Kano.
Gwamna Abba ya kara da cewa kasafin kudin shekarar 2026 “ba wai tsare-tsaren kudi ne kawai ba, har ila yau yarjejeniya ce domin kammala ayyuka, karfafa nasarorin da aka samu, da gina tsarin da zai amfanar da al’umma a nan gaba.”
Ya ce kudirin kasafin kudin “na da buri mai girma amma a hankali aka tsara shi,” wanda ke nuna nufin gwamnatin sa ta gina Kano mai dorewar ci gaba, fadada damammaki, da kyautata rayuwar jama’a.
Gwamnan ya kuma jinjinawa ’yan majalisar dokoki bisa goyon bayan da suka bayar a shekarar 2025, musamman wajen mayar da hankali kan bukatun jama’a.
A cikin kasafin kudin, an ware N934,640,032,101.00 domin ayyukan raya kasa, yayin da N433,487,897,170.00 suka tafi ga kudaden gudanarwa. Fannin ilimi ne ya fi samun kaso mafi yawa, inda aka ware N405,350,318,751.17, wanda ya kai kashi 30 cikin 100 na kasafin.
