Connect with us

News

Kungiyar Iyayen Ɗaliban MAAUN Sun Fasa Kwai Kan Koken PCACC, Ta Kare Mutuncin Jami’ar

Published

on

FB IMG 1747143642210

Kungiyar Iyayen Ɗaliban Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Alhaji Mustapha Balarabe, ta nesanta kanta daga koke da aka kai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano (PCACC), tana mai cewa lamarin sharri ne da kuma ƙoƙarin bata suna.

A cikin wata sanarwa da shi da sakatariyar kungiyar, Hajiya Habiba Sarki suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana rahotannin kafafen yada labarai da suka alakanta jami’ar da “tsauraran kudaden yaye dalibai” a matsayin kuskure mai nasaba da rashin gaskiya.

Advertisement

MAAUN Parents Association Condemns Petition to PCACC, Affirms University’s Autonomy

Shugaban ya ce: “MAAUN na daga cikin jami’o’in kudi mafi araha a Kano, tana ba da ingantaccen ilimi da katafaren tsari. Wasu jami’o’in kudi a Kano na cajin kudaden karatu sau uku fiye da MAAUN, amma ba a jin koke-koken jama’a a kansu. Don me ake niyya kan MAAUN?”

Ya ci gaba da cewa biyan kuɗin yaye dalibi ba sabon abu ba ne a jami’o’in kudi, tare da bayyana koke da aka shigar a matsayin “shirin bata suna daga wani mutum marar suna da ke ikirarin kare dalibai da iyaye.”

Advertisement

“Me ya haɗa MAAUN da Hukumar Karɓar Korafe-korafe ta Jama’a? Wannan abu sharri ne tsagwaro,” in ji shi.

Kungiyar ta kuma yabawa wanda ya kafa jami’ar bisa jajircewa da kishin kasa, musamman yadda ya tsaya tsayin daka wajen daidaita kudaden karatu duk da matsin tattalin arzikin da ya sa wasu jami’o’i ƙara kuɗi.

Advertisement

Ta kuma jaddada cewa MAAUN za ta ci gaba da kare ingancin ilimi da mutuncin ta, tare da tabbatar da cewa dalibai da iyaye suna samun sahihin bayani kan duk wata matsala.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending