News
Sama Da Mutane Miliyan 24 Sun Kamu Da Cutar Malariya Cikin 2025 A Najeriya — Gwamnatin Tarraya
Sabon rahoto daga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ya nuna cewa mutane miliyan 24.47 ne suka kamu da zazzabin cizon sauro a Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2025.
Rahoton, wanda aka wallafa a Rahoton Kididdigar Lafiya na Kasa 2025, ya bayyana cewa adadin masu zuwa asibitoci da zazzabi da ake gwada su da Rapid Diagnostic Test (RDT) ko binciken dakin gwaje-gwaje na karuwa a hankali, kuma cutar malariya na karuwa kowane zangon shekara.
Ƙididdigar Watanni Uku-uku:
Janairu – Maris: An gwada mutane 10.5m, 7.3m daga cikinsu sun fito da sakamakon cewa sun kamu.
Afrilu – Yuni: Mutane 11.4m aka gwada, 7.8m sun tabbatar da kamuwa.
Yuli – Satumba: An gwada 12.8m, inda 9.3m aka tabbatar da cutar.
Jimillar wadanda aka gwada cikin watanni tara sun kai 34.8m, yayin da 24.47m aka tabbatar da malariya.
Haka zalika, adadin masu neman maganin Artemisinin-based Combination Therapy (ACT) ya karu, inda 23.85m suka samu magani a wannan lokaci.
Masana lafiyar sun ja hankalin cewa jinkirin zuwa asibiti, karancin cibiyoyin lafiya masu inganci, da yanayin damina da ke karfafa hayayyafar sauro, na daga cikin dalilan da ke kara yawan kamuwa da cutar.
