Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da ’Yan Sanda Daga Tsaron Manyan Mutane A Najeriya

Published

on

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Advertisement

Dalibai 50 Daga Cikin Wanda Aka Sace Sun Kuɓuta Daga Hannun Masu Garkuwa A Neja

Onanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda.

An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS.

Advertisement

Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne, ya nemi jami’an tsaro daga Hukumar NSCDC maimakon ’yan sanda.

Najeriya ba ta da isassun ’yan sanda a yankunan karkara, kuma hakan yana haifar da tsaiko wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Advertisement

Saboda haka Shugaba Tinubu, ya umarci a ƙara yawan ’yan sandan da ke bai wa jama’a tsaro.

Onanuga, ya kuma ce Shugaban Ƙasa ya amince da ɗaukar ƙarin sabbin ’yan sanda 30,000.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin inganta cibiyoyin horas da ’yan sanda a faɗin Najeriya.

Taron tsaron da aka gudanar a ranar Lahadi, ya samu halartar Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da Darakta-Janar na DSS, Tosin Adeola Ajayi.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending