News
Ana Zargin Wani Jami’in Tsaron Gidan Gyaran Hali Da Lalata Da Fursuna Har Ta Dauki Ciki A Potiskum
Ana zargin wani jami’in tsaron gidan gyaran hali da ke Potiskum a Jihar Yobe da aikata lalata da wata fursuna, lamarin da ya janyo ta samu ciki mai watanni kusan bakwai.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’in, Sani Saleh-Bodejo, mai mukamin ASC II, ya aikata laifin ne a cikin sashin mata na gidan gyaran halin tare da goyon bayan wata jami’ar da ke kula da bangaren.
Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da ’Yan Sanda Daga Tsaron Manyan Mutane A Najeriya
Fursunar da ake zargin an yi wa fyaden, Blessing Sunday, likitoci sun tabbatar tana da ciki mai makonni 27.
Majiyoyi daga cikin hukumar sun bayyana cewa ana zargin wasu manyan jami’an hukumar da kokarin rufe batun, har ma da yunkurin ganin an zubar da cikin da fursunar ke dauke da shi, duk kuwa da hadarin da hakan ka iya jawo mata.
Wata majiya ta shaida cewa an riga an mika rahoton lamarin ga Shugaban Hukumar Gyaran Hali na Kasa na Zone R, ACG Adamu Yahaya.
Rahoton farko da aka gabatar ya nuna cewa Blessing ta kai kusan watanni uku da rabi da ciki lokacin da aka fara bayyana zargin fyaden.
Majiyoyi sun ce an gudanar da wani taro tsakanin shugaban gidan gyaran halin da mahaifin Blessing, wanda ake zargin manufarsa ita ce rufe maganar.
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa an tura wasu daga cikin jami’an da ake zargi zuwa wasu sabbin wuraren aiki, ciki har da tura Sani Bodejo zuwa cibiyar kula da hukuncin non-custodial da ke Jakusko, Yobe.
Jaridar Daily Nigerian ta tuntubi kwamandan hukumar a Yobe, Abdullahi Ibrahim, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan lamarin kafin ya katse wayar. ACG Zone R, Adamu Yahaya, ya ki yin tsokaci.
Kakakin hukumar a Yobe, Abdullahi Adamu, ya ce hukumar za ta gudanar da cikakken bincike sannan ta fitar da sanarwa a hukumance.
-
News4 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News5 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News7 days ago
“Wasu Daga Cikin Mutanen Da Buhari Ya Amince Da Su Ne Suka Ci Amanarsa” — Lawal Daura
