Connect with us

News

‎Wata Amarya Ta Yi Alajin Angonta Kwanaki Uku Bayan Ɗaura Auren Su A Katsina  ‎

Published

on

Wata sabuwar amarya a Jihar Katsina, Zainab Muhammad, ta kashe mijinta, Abubakar Abdurrahman, bayan kwana uku da ɗaura auren su a garin Jibia.

‎Rahotanni sun nuna cewa an ɗaura auren ne ranar Alhamis, amma lamarin ya faru a jiya da rana a cikin gidan ma’auratan, inda ake zargin Zainab ta yanka mijinta har lahira.

Advertisement

Ƴan Ta’adda Sun Sace Mata Manoma 13 A Borno

‎Wani maƙwabcin su ya shaida lamarin ya ce afkuwar kisan ta jefa al’umma cikin ruɗani, inda ake ta ta baba akan lamarin domin neman amsa kan abin da ya faru.

‎Mai unguwar yankin ya shaida cewa tun kafin auren, an san Zainab na fama da matsalolin da suka shafi aljanu, wanda a cewarsa hakan na iya zama dalilin da ya haifar da kisan.

Advertisement

‎Marigayin Abubakar an binne shi ne da yamma, misalin ƙarfe 5, bisa tsarin Musulunci.

‎Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama amaryar, tare da fara bincike kan musabbabin kisan da yadda lamarin ya faru.

Advertisement

 

DAILY REALITY

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending