News
Wata Amarya Ta Yi Alajin Angonta Kwanaki Uku Bayan Ɗaura Auren Su A Katsina
Wata sabuwar amarya a Jihar Katsina, Zainab Muhammad, ta kashe mijinta, Abubakar Abdurrahman, bayan kwana uku da ɗaura auren su a garin Jibia.
Rahotanni sun nuna cewa an ɗaura auren ne ranar Alhamis, amma lamarin ya faru a jiya da rana a cikin gidan ma’auratan, inda ake zargin Zainab ta yanka mijinta har lahira.
Wani maƙwabcin su ya shaida lamarin ya ce afkuwar kisan ta jefa al’umma cikin ruɗani, inda ake ta ta baba akan lamarin domin neman amsa kan abin da ya faru.
Mai unguwar yankin ya shaida cewa tun kafin auren, an san Zainab na fama da matsalolin da suka shafi aljanu, wanda a cewarsa hakan na iya zama dalilin da ya haifar da kisan.
Marigayin Abubakar an binne shi ne da yamma, misalin ƙarfe 5, bisa tsarin Musulunci.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama amaryar, tare da fara bincike kan musabbabin kisan da yadda lamarin ya faru.
