News
Ana Zargin ‘Yan Bindiga Sun Sace Budurwa Sa’o’i Kadan Kafin Daurin Aurenta A Sokoto
Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno a jihar Sokoto, inda suka yi garkuwa da amarya,kwaayenta da wasu daga cikin mahallara taron.
Lamarin ya faru ne daren Asabar bayan da maharan suka shiga kauyen kusan ƙarfe Daya na dare, suka soma harbe-harbe kafin su kwashe mutane.
Rahotanni daga yankin sun ce mata da dama da suka taru domin taimakawa amaryar wajen shirye-shiryen bikinta suma an sace su.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Isah Sadeeq Achida, ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya ce ba zai tabbatar ko amaryar na cikin wadanda aka sace ba, saboda ba a tantance adadin mutanen da aka dauke ba tukuna.
Daily Post ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Rufai, amma bai amsa kiran waya ba
Harin ya faru ne awanni kaɗan bayan da aka ce an biya kudin fansa na Naira miliyan huɗu da babur guda domin sako wasu da aka sace a garin Rabah.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
