Connect with us

News

Mutum Biyar ’Yan Gida Ɗaya Sun Rasu Sakamakon Tashin Gobara A Katsina 

Published

on

Spread the love

Wata mummunar gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta yi ajalin mutum biyar ’yan gida ɗaya a unguwar Kofar Sauri, cikin birnin Katsina.

Shaidu a yankin sun ce gobarar ta kama gidan ne cikin dare, inda ta bazu cikin sauri har ta ƙone dukkan sassan gidan kafin maƙwabta su samu damar shiga domin kai agaji. Iyalan da suka rasu sun haɗa da uba, uwa da ’ya’yansu uku, waɗanda suka makale a cikin gidan lokacin da wutar ta yi ƙamari.

Gwamnonin Arewa Sun Bukaci A Dakatar Da Ayyukan Hako Ma’adanai Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro

Wasu mazauna yankin sun ce gobarar na iya samo asali ne daga matsalar wutar lantarki da aka dawo da ita a lokacin, sai dai wasu suna ganin iska mai ƙarfi da ta kad’a na iya taimakawa wajen bazuwar wutar cikin sauri.

Har yanzu hukumomin ’yan sanda da na kashe gobara na jihar, da ma na tarayya, ba su fitar da cikakkiyar sanarwa kan musabbabin faruwar lamarin ba, ko matakan da ake ɗauka na gaggawa domin bincike.

Advertisement

 

 

LEADSHIP

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *