News
Hukumomin Tsaron Ghana Sun Kama ‘Yan Najeriya 32 Bisa Zargin Damfara Ta Yanar Gizo
Hukumomin tsaron kasar Ghana sun ce sun kama ‘yan Najeriya 32 a wani samame da suka kai a yankin Tuba da ke Kasoa, bisa zargin hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo.
Hukumar Cyber Security Authority (CSA) ta Ghana, tare da hadin gwiwar jami’an Tsaron Kasa, ta bayyana cewa samamen ya gudana ne da safiyar Asabar, 13 ga Disamba, 2025, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da ake zargin mutanen ke gudanarwa.
An Gurfanar Da Mutum 3 A Kotu Kan Zargin Satar Kaji 500 Da Darajarsu Ta Kai Naira miliyan 9
A cewar hukumar, ana zargin mutanen da shiga damfarar da Sunan soyayya (romance scam), inda suka kafa wata cibiyar damfara ta yanar Gizo a maboyarsu da ke Tuba.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun kwace kwamfutoci 31 da wayoyin hannu 15, waɗanda ake kyautata zaton an yi amfani da su wajen aikata laifukan da ake zargi.
An ce an mika kayayyakin da aka kwato zuwa sashen binciken fasaha domin duba bayanai da tantance su, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Hukumar CSA ta ce mutanen da aka kama na hannun ‘yan sanda, kuma suna bayar da hadin kai ga jami’an bincike.
A cewar hukumar, wannan mataki na daga cikin kokarin da Ghana ke yi na dakile laifukan yanar gizo, tare da kare tsarin sadarwa da tsaron dijital na kasar.
Ministan Sadarwa, Fasahar Dijital da Kirkire-kirkire na Ghana, Samuel Nartey George, ya yaba wa hukumar CSA, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da mara mata baya wajen yaki da laifukan intanet.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ministan ya ce:
“Wannan samame wani muhimmin mataki ne na yaki da damfara ta yanar gizo.
