News
Dan Kunar Bakin Wake Dauke Da Kayan Hada Bam Ya Shiga Hannun Sojoji A Maiduguri
Sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun kama wani mutum da ake zargin ɗan kunar bakin wake ne ɗauke da kayan hada bam a babban Masallacin Juma’a na garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Talata 30 ga Disamba 2025.
Sanarwar ta ce sojojin sun cafke mutumin ne da misalin ƙarfe 5:40 na yamma bayan samun bayanan sirri, inda aka same shi dauke da sassan bam da aka riga aka shirya, abin da ke nuna yiwuwar shirin kai hari.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna mutumin ɗan Karamar Hukumar Bama ne, kuma ana ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano masu ɗaukar nauyinsa da sauran mutanen da ke da alaƙa da ayyukan ta’addanci a yankin.
A wani ci gaban, sojojin sun kama wata mota a kofar kan iyakar Kamaru da Najeriya dauke da buhunhuna shida na takin urea da ake amfani da shi wajen hada bam, inda daga bisani aka sake gano wasu buhunhuna shida bayan kama dillalin takin, wanda ya kai jimillar buhunhunan da aka kwace goma sha biyu.
