News
Ranar Alhamis Dokar Haraji Za Ta Fara Aiki — Shugaba Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa babu makawa a ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2026, sabbin dokokin haraji za su fara aiki.
Tinubu a wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, ya yi fatali da zargin cewa za a yi sauye-sauye ga dokokin, don haka dokokin za su fara aiki kamar yadda aka tsara, babu gudu babu ja da baya.
Barayi Sun Sace Yuro Miliyan 30 Kwatankwacin Naira Bliyan 51 A Wani Banki
Wannan na zuwa ne duk da adawar mafin yawan ’yan Najeriya suka nuna tare da zargin cushe a sabbin dokokin harajin masu cike da rudani.
’Yan Majalisar Wakilai na zargin an yi aringizo a dokokin da babban zauren majalisa ya abince da su kafin a sanya a kundin dokokin gwamnati, a yayin da kungiyar lauyoyi da kungiyar kwararrun akantoci da masana harkar haraji suka nuna hadari da saba wa kundin tsarin mulki da ke tattare da aiwatar da sabbin dokokin.
Tinubu ya ce wasu daga cikin matakan sun fara aiki tun a Yuni 2025, kuma an tsara su ne domin gina “hanyoyin tara kuɗi mai adalci, gasa da ƙarfi” ga ƙasar.
A cewarsa, ba don ƙara haraji aka yi dokokin ba, sai dai don sake daidaita tsarin, daidaita ƙa’idoji da kuma ƙarfafa yarjejeniyar zamantakewa.
Ya ce, “Gwamnatinmu tana sane da maganganun jama’a kan zargin sauye-sauye a wasu sassan sabbin dokokin haraji,” in ji Tinubu, amma ya ce, “Ba a tabbatar da wata matsala mai muhimmanci da za ta iya dakatar da tsarin gyaran ba.”
Ya roƙi masu ruwa da tsaki da su goyi bayan aiwatarwa da dokokin, wanda ya ce yanzu ya shiga matakin karshe.
Ya ƙara da cewa amincewa da gwamnati za ta ginu ne “ta hanyar yanke sahihan hukunci, ba ta hanyar matakan gaggawa da ba su dace ba.”
Tinubu ya sake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa ga bin doka da oda, tare da alkawarin yin aiki tare da Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin warware duk wata matsala da ka iya tasowa.
Shugaban ƙasar ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki “a bisa maslahar jama’a gaba ɗaya domin tabbatar da tsarin haraji da zai tallafa wa bunƙasar tattalin arziki da kuma ɗaukar nauyi tare.”
Ana kallon waɗannan gyare-gyaren a matsayin wani ɓangare na babban shirin tattalin arzikin Tinubu domin daidaita kuɗaɗen Nijeriya da jawo jari daga kasashen waje, bayan shekaru na matsin tattalin arziki da dogaro da kuɗaɗen mai.
