News
Barayi Sun Sace Yuro Miliyan 30 Kwatankwacin Naira Bliyan 51 A Wani Banki
Barayi sun fasa wani reshen bankin Sparkasse da ke birnin Gelsenkirchen a yammacin Jamus, inda suka sace kuɗi da dukiya da darajarsu ta kai Yuro miliyan 30, kwatankwacin Naira biliyan 51, a cewar ’yan sanda.
Lamarin ya faru ne a lokacin hutun bukukuwan Kirsimeti, lokacin da yawancin bankuna ke rufe, abin da ya bai wa barayin damar aiwatar da fashin ba tare da an lura ba.
Rahotanni sun ce barayin sun hako rami ta cikin katangar siminti mai kauri, suka shiga ma’adanar bankin, inda suka fasa dubban akwatunan ajiyar abokan hulɗa, suna kwashe kuɗi da kayan ado masu daraja.
’Yan sanda sun bayyana cewa akalla mutane 2,500 da ke mu’amala da bankin ne lamarin ya shafa, inda da dama ke ajiyar kuɗin ritaya da dukiyar iyalansu a cikin akwatunan ajiyar.
Ba a gano fashin ba sai da ƙararrawar gobara ta bankin ta tashi da asubahin Litinin, 29 ga Disamba, lamarin da ya ja hankalin jami’an tsaro.
A safiyar Talata, wasu daga cikin abokan hulɗar bankin sun taru a gaban reshen bankin, suna nuna fushinsu kan rashin samun cikakken bayani daga mahukuntan bankin game da asarar da aka yi.
’Yan sanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata fashin.
