Connect with us

News

Yadda Wasu Hasalallun Matasa Suka Babbake Ofishin NSCDC A Kano

Published

on

Spread the love

 

Rundunar Kare Kadarorin Gwamnati da Al’umma (NSCDC) reshen jihar Kano ta tabbatar da kai hari ofishinta da ke Danmaje, a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da ake zargi tare da lalata ginin ofishin ta hanyar cinna masa wuta.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa harin ya faru ne ƙasa da awanni 24 bayan wani makamancin haka da aka kai wa rundunar NSCDC a jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku.

Dan Kunar Bakin Wake Dauke Da Kayan Hada Bam Ya Shiga Hannun Sojoji A Maiduguri

Mai magana da yawun NSCDC a Kano, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin a Kano. Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Lahadi, lokacin da mazauna garin Yansango suka kawo wasu mutane uku da ake zargin ɓarayin adaidaita sahu (babur mai ƙafa uku) zuwa ofishin rundunar da ke Danmaje.

Advertisement

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne a wani wuri da ya yi ƙaurin suna wajen fashin babura. Sai dai kafin rundunar ta fara gudanar da bincike a kansu, wasu gungun mutane daga Yansango, Madinawa, Gagarawa, Limawa, Yankatsari, Danmaje da Gurjiya suka mamaye ofishin NSCDC.

Abdullahi ya ce gungun mutanen sun nemi a miƙa musu mutanen uku domin su yi musu hukunci da kansu. “Lamarin ya ta’azzara ne bayan da gungun mutanen suka cika ofishin rundunar,” in ji shi. “Kafin a samu damar turo ƙarin jami’ai, mutanen sun kutsa cikin ofishin, suka cinna masa wuta tare da yanka mutanen ukun.”

Ya ƙara da cewa, yayin da wasu jami’an NSCDC da ke bakin aiki suka samu nasarar tserewa daga ginin da ke ci da wuta, jami’ai uku sun jikkata, kuma a halin yanzu suna ci gaba da karɓar magani.

Rundunar NSCDC ta yi kira ga al’ummar Dawakin Kudu da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu, tana mai jaddada cewa hukuma ce kaɗai ke da alhakin tabbatar da doka da oda.

Advertisement

A halin da ake ciki, Kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Agalama, bisa wakilcin Kwamandan-Janar na ƙasa, ya kafa wani kwamiti domin gudanar da cikakken bincike kan harin.

Abdullahi ya jaddada cewa rundunar za ta tabbatar da an yi adalci, inda ya ce ana ƙoƙarin gano tare da kama duk waɗanda ke da hannu wajen lalata ofishin da kuma kashe mutanen ukun.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *