News
Najeriya Na Bin Togo, Benin Da Nijar Bashin Kudin Wutar Lantarki Da Adadinsu Ya Haura Naira Biliyan 25
Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce ƙasashen Togo, Jamhuriyar Benin da Jamhuriyar Nijar ,Najeriya na bin su bashin kuɗin wutar lantarki da ya kai dalar Amurka miliyan 17.8, wanda ya yi daidai da sama da Naira biliyan 25 bisa farashin canjin kuɗi na yanzu.
A cikin rahotonta na zangon uku na shekarar 2025, NERC ta bayyana cewa Hukumar Kasuwar Wutar Lantarki (Market Operator) ta caje waɗannan ƙasashe jimillar dalar Amurka miliyan 18.69 kan wutar da aka ba su a lokaci.
Majalisar Dokokin Ribas Ta Sake Fara Yunƙurin Tsige Gwamna Siminalayi Fubara
Sai dai, an ce sun biya dalar Amurka miliyan 7.125 kacal, lamarin da ya bar bashin dalar Amurka miliyan 11.56.
Hukumar ta kuma ce akwai tsofaffin basussuka da aka tara tun a zangonni da suka gabata, inda aka bayyana cewa an biya dalar Amurka miliyan 7.84 daga cikin dalar Amurka miliyan 14.7, wanda ya bar ragowar dalar Amurka miliyan 6.23.
Idan aka haɗa bashin tsohon da na zangon uku na 2025, adadin ya kai dalar Amurka miliyan 17.8, wanda ke nuni da kusan Naira biliyan 25.36 bisa musayar Naira 1,425 kan kowace dala.
NERC ta bayyana cewa kamfanonin da ke karɓar wutar lantarkin daga Najeriya sun haɗa da Compagnie Énergie Électrique du Togo, Société Béninoise d’Énergie Électrique ta Benin, da kuma Société Nigérienne d’Électricité ta Nijar.
Rahoton ya nuna cewa matakin biyan kuɗin da ƙasashen ukun suka yi bai wuce kashi 38.09 cikin 100 ba a zangon na uku, abin da ke nuna cewa fiye da rabin bashin ya ci gaba da zama a wuyan su zuwa ƙarshen lokacin.
