Connect with us

News

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Yi Ajalin Mutane 10, Ciki Har da Kansila A Taraba 

Published

on

images 13

Aƙalla mutane 10 ne ake zargin sun rasa rayukansu, ciki har da kansilar mazaɓar Akete a ƙaramar hukumar Donga ta jihar Taraba, sakamakon wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wani ganau, Lawal Adamu, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa rikicin ya fara ne a ranar Asabar a ƙauyen Gundom, bayan da wani makiyayi ya lalata wata gona. A cewarsa, fusata da lamarin ya sa wasu mazauna ƙauyen suka kama makiyayin tare da kashe shi, abin da ya haifar da ramuwar gayya tsakanin ɓangarorin biyu.

Advertisement

Dan Jarida A Kano Aminu Abdullahi Ya Shirya Horarwa Da Raba Audugar Mata Kyauta.

“Bayan kisan makiyayin ne rikicin ya ɓarke sosai, inda aka shiga faɗa tsakanin manoma da makiyaya,” in ji Lawal.

Ya ce, duk da cewa ana hasashen aƙalla mutane 10 ne suka mutu, amma ba zai iya tantance ainihin adadin waɗanda suka rasa rayukansu daga ɓangarorin da suka yi artabu ba.

Advertisement

A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ƴansandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Sai dai ya ce zuwa yanzu, ƴansanda sun gano gawar mutane uku ne kawai, tare da wata mata guda da ta samu rauni.

Mshelizah ya ƙara da cewa baturen ƴansandan Donga ya jagoranci jami’ansa zuwa dazukan da ke kewaye da yankin domin ci gaba da bincike, don gano sahihin adadin waɗanda rikicin ya shafa da kuma gano waɗanda suka tsere.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending