News
FRSC Ta Cafke Mutumin Da Ke Yi Wa Jami’anta Sojan Gona Yana Ƙwace Babura A Kano
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta ce ta cafke wani mutum da ake zargi da yin wa jami’anta sojan gona, inda yake ƙwace babura daga hannun jama’a a wasu sassan jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na FRSC a Kano, Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa an cafke mutumin ne bayan da hukumar ta samu korafe-korafe daga al’umma dangane da mutane da ke fakewa da sunan FRSC suna yin sintiri ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, wanda ake zargin mai suna Abdullahi Ali, ɗan ƙauyen Bela ne da ke ƙaramar hukumar Ungoggo, kuma an cafke shi a ranar 19 ga Janairun 2026.
FRSC ta ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana amfani da ƙarfi wajen ƙwace babura, kuma ana zargin wasu daga cikin baburan da aka ƙwace sun ɓace kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Hukumar ta kuma ce an samu lasisin tuƙi na bogi a hannun mutumin a lokacin da aka cafke shi, abin da ke nuna amfani da takardun ƙarya wajen aikata laifuka.
FRSC ta jaddada cewa ba ta ba kowa izinin yin mata sojan gona ba, tare da kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani mutum da ke fakewa da sunanta ga hukumomin tsaro.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
