News
An Harbi Wata Mata Kan Kin Biyan Haraji A Kogi

Wata mata mai suna Facilla, a Jihar Kogi ta sha dalma bayan hatsaniya ta kaure tsakaninta da masu karɓar harajin gawayi a yankin Agbede na ƙaramar hukumar Kabba.
Rahotanni sun bayyana cewa masu karɓar harajin sun samu ’yar taƙaddama tsakaninsu da matar, lamarin da ya yi sanadiyar ɗaya daga cikinsu zaro bindiga ya harbe ta, inda ta damu mummunan raunuka.
An Biya Wanda Aka Daure Bisa Kuskure Diyar Sama Da Naira Biliyan 2
Tuni dai aka miƙa matar zuwa asibitin ƙwararru na jihar domin ba ta agajin gaggawa kamar yanda Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ta Kabba da lamarin ya faru ya sha alwashin binciko tare da hukunta mutanen da suka yi wannan aika-aika.
-
News4 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
