Connect with us

News

SERAP Ta Maka Ministan Wutar Lantarki Da NBET Kotu Kan Zargin Badakalar N128bn 

Published

on

‎Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da sa ido kan kashe kuɗaɗen gwamnati, a Najeriya, SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya NBET, bisa zargin karkatar da Naira biliyan 128.

‎A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan zarge-zargen da ke cikin rahoton Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da aka wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025.

Advertisement

Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Dodanni Uku A Akwa Ibom

‎Ƙungiyar na neman kotu ta tilasta wa waɗanda ake ƙara su yi cikakken bayani kan kuɗin, tare da bayyana sunayen jami’ai ko kamfanonin da suka amfana da su.

Advertisement

‎A cewar SERAP, cin hanci da rashawa a ɓangaren wutar lantarki na ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin duhu, inda ake fama da rushewar layin wuta da kuma biyan kuɗaɗen wuta masu tsada.

SERAP ta kuma ambaci tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa na yaƙi da cin hanci, tana mai cewa hukumomin gwamnati na da wajibi na bin gaskiya da riƙon amana.

Advertisement

‎Sai dai har yanzu ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending