Connect with us

News

Wasu Tsofaffin ‘Yan Majalisa Sun Ce Ba Sa Goyon Bayan Shugaba Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara

Published

on

Tinubu

Wasu tsofaffin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa 17 sun bayyana cewa ba su da hannu a wani taron da aka shirya domin nuna goyon baya ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na sake tsayawa takara a wa’adi na biyu.

‎Wannan na zuwa ne bayan da Ƙungiyar Tsofaffin ’Yan Majalisa ta Ƙasa (NFFL) ta sanar da mara wa Tinubu baya a wani taro da aka gudanar ranar Asabar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Advertisement

Gwamnatin Kano ta buɗe sabon aikin magudanar ruwa a Unguwar Badawa

‎An ce Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar wasu fitattun tsofaffin ’yan majalisa daga jam’iyyu daban-daban.

Advertisement

‎Daga cikin mahalartan taron akwai tsofaffin Shugabannin Majalisar Dattawa Pius Anyim da Ken Nnamani, da kuma tsofaffin Kakakin Majalisar Wakilai Patricia Etteh da Yakubu Dogara, da sauransu.

‎Sai dai a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da tsofaffin ’yan majalisar suka fitar ranar Asabar, sun ce ba su halarci taron ba, kuma ba su amince da duk wani goyon baya da aka ce an bayar da sunayensu.

Advertisement

‎Sun bayyana taron a matsayin wanda ba ya wakiltar ra’ayin dukkan tsofaffin ’yan majalisa a faɗin ƙasar.

‎A cewarsu, idan gwamnati na neman wa’adi na biyu, ya kamata ta gabatar da hujjoji kan batutuwan tsaro, tattalin arziki, samar da ayyukan yi da rage tsadar rayuwa.

Advertisement

‎Daga cikin waɗanda suka sanya hannu a sanarwar akwai Hon. Sergius Oguns, Hon. Herman Hembe, Hon. Sam Okwu, Hon. Zakari Mohammed, Hon. Tom Zakari, Hon. Mohammed Soba, Hon. Chika Adamu, Hon. Sadiq Ibrahim da Hon. Tajudeen Ajagbe, da wasu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending