Connect with us

News

Jami’an Yan Sanda Sun Kama Mutane 21 Da Ake Zargin Da Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba A Zamfara

Published

on

images (5)

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama mutane 21 da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a wani sumame da aka gudanar a ƙananan hukumomin Zurmi da Maradun na jihar.

Kakakin ’yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce kamen ya biyo bayan wani sumame na haɗin gwiwa da aka kai ranar Asabar da jami’an Sashen Yaƙi da Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida ba, Sashen Ayyuka na Musamman, da Sashen Lalata Bama-bamai na rundunar.

Advertisement

Kamfanin Best Medix 24 Pharmacy Yayi Bikin Cika Shekaru 4, Ka Kuma Karrama Ma’aikatansa Da Kyaututtukan Alfarma

An gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro da Kare Rayuka ta Farar Hula (NSCDC) da kuma jami’an Ma’aikatar Ma’adanai da Bunƙasa Albarkatu ta Tarayya, Ofishin Gusau.

Advertisement

A cewar Abubakar, tawagar ta kai sumame ne a ƙauyen Boko da ke Zurmi LGA da kuma ƙauyen Kaya da ke Maradun LGA, bayan samun rahotannin ci gaba da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan.

“An aiwatar da sumamen cikin nasara, wanda ya kai ga kama mutane 21 da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

“Yanzu haka ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargin a Sashen Ayyukan Task Force kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida ba,” in ji shi, yana ƙara da cewa za a sanar da ƙarin bayani yayin da bincike ke gudana.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending