News
Dan’agundi Ya Taya Nasir Jao’ji Murna Kan Nadinsa Daraktan City Boy Movement a Kano
Daraktan Janar na Cibiyar Kula da Inganta Ayyuka ta Ƙasa (NPC) kuma Darakta Janar na Tinubu Support Group na Arewa maso Yamma, Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ya taya Hon. Nasir Bala Aminu Jao’ji murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin Daraktan City Boy Movement na Jihar Kano.
Dr. Dan’agundi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, wadda aka aikowa kafar labarai a Kano, inda ya bayyana nadin a matsayin wanda ya dace kuma aka yi shi a lokacin da ya dace.
Ƙasar Saudiyya Ta Sanar Da Shirinta Na Fara Bai Wa Miliyoyin Raƙuman Da Ke Ƙasar Fasfo
A cewarsa, an bai wa mutumin da ya cancanta wannan muƙami, la’akari da irin ƙwarewa da Hon. Jao’ji ke da ita wajen haɗa jama’a daga tushe, tare da kyakkyawar alaƙarsa da al’umma a matakin ƙasa.
Sanarwar ta ce Dr. Dan’agundi ya jaddada cewa nadin zai taimaka wajen ƙarfafa sabuwar tafiyar City Boy Movement a Kano, tare da ba da gudummawa wajen yaɗa manufofin jam’iyya da shugabanci a tsakanin matasa da masu ruwa da tsaki.
Ya ƙara da cewa Tinubu Support Group za ta ci gaba da bai wa City Boy Movement cikakken goyon baya domin ƙarfafa aiwatar da Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Dr. Dan’agundi ya kuma bai wa Hon. Nasir Jao’ji tabbacin cikakken haɗin kai da goyon bayan ƙungiyar, domin tabbatar da nasarar aikinsa da ci gaban tafiyar a fadin Jihar Kano.
