News
Sama Da Mutum 167,000 Ne Suka Kammala Rajistar Katin Zaɓe A jihar —Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa sama da mutane 167,000 ne suka kammala rajistar katin zaɓe a jihar tun daga watan Agustan 2025 zuwa yanzu, yayin da ta sanya sabon buri na rajistar sabbin masu kaɗa ƙuri’a miliyan huɗu gabanin zaɓen shekarar 2027.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida nana jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce waɗanda suka yi rajistar a halin yanzu suna jiran karɓar katunan zaɓe na dindindin (PVC).
Waiya ya bayyana adadin a matsayin mai ƙarfafa gwiwa, amma ya jaddada cewa har yanzu bai kai matsayin yawan masu zaɓe da jihar Kano ke da shi ba, lamarin da ke buƙatar ƙarin wayar da kan jama’a domin cimma burin miliyan huɗu da aka sanya.
A cewarsa, domin hanzarta aikin rajistar zaɓe da karɓar PVC, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin wayar da kai na musamman tun a watan Agustan 2025, wanda ke da alhakin jan hankalin al’umma kan muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya.
Kwamitin, a cewarsa, ya ƙunshi jami’an gwamnati da suka haɗa da kwamishinoni, masu ba gwamnati shawara na musamman, wakilan Hukumar Hisbah, Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Nijeriya (NUJ), Ƙungiyar Mata ‘Yan Jaridu (NAWOJ), Ƙungiyar Daliban Nijeriya (NANS) da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwamishinan ya ce an ɗora wa kwamitin nauyin zagayawa dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, da nufin tabbatar da cewa akalla mutane miliyan huɗu daga Kano sun yi rajista kuma sun shirya kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.
Baya ga batun rajistar Katin zaɓe, Waiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiwatar da ayyukan raya kasa sama da 900 a sassa daban-daban na Kano, inda ya ce an rarraba ayyukan yadda ya dace domin bunƙasa ci gaba da inganta jin daɗin al’umma.
