Connect with us

News

Wasu Bata Gari Sun Kai Hari Hedikwatar Jam’iyyar ADC

Published

on

images (6)

Wasu ‘yan daba sun kai hari hedikwatar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Edo a daren Laraba, inda suka lalata wasu kadarorin jam’iyyar tare da yin yunkurin ƙona ginin.

Rahotanni sun ce harin ya auku ne a hedikwatar jam’iyyar da ke kan titin Ogbelaka a Birnin Benin. Mazauna yankin sun ce sun kai ɗauki bayan da suka lura da abin da ke faruwa, lamarin da ya hana wutar kama ginin.

Advertisement

Sama Da Mutum 167,000 Ne Suka Kammala Rajistar Katin Zaɓe A jihar —Gwamnatin Kano

A wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, wani mutum da ke ikirarin kasancewa mamba a jam’iyyar ADC ya nuna tagogi da na’urorin tsaro na CCTV da suka lalace sakamakon harin.

Advertisement

Mutumin ya zargi jam’iyyar APC mai mulki a jihar da hannu a lamarin, duk da cewa bai gabatar da wata hujja ba. Jam’iyyar APC ba ta ce komai kan zargin ba a lokacin hada wannan rahoto.

Shugabar jam’iyyar ADC a Jihar Edo, Kennedy Odion, ta tabbatar da faruwar harin, tana mai cewa maharan sun zo da niyyar ƙona ginin hedikwatar.

Advertisement

Ta ce an lalata tagogi da wasu kayayyaki kafin magoya bayan jam’iyyar da ke yankin su dakile harin. Ta kuma ce an gano wani gwangwani da ke dauke da fetur, wanda ake zargin an kawo ne domin kunna wuta.

A cewar ta, jam’iyyar ADC na fuskantar matsin lamba yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, saboda yadda take kara samun karɓuwa a matsayin jam’iyyar adawa.

Advertisement

Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta tabbatar da faruwar lamarin. Mai magana da yawun rundunar, Eno Ikoedem, ta ce an samu rahoton harin ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Laraba.

Ta ce jami’an tsaro sun isa wurin domin dawo da zaman lafiya, yayin da bincike ke ci gaba don gano tare da cafke waɗanda suka aikata harin.

Advertisement

ADC na daga cikin jam’iyyun siyasa da ke neman kara bayyana a siyasar Najeriya, musamman gabanin zaɓen 2027, inda ta jawo hankalin wasu fitattun ‘yan siyasa daga manyan jam’iyyun kasar.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending