Connect with us

News

Yan Jarida 14 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Bauchi

Published

on

IMG 20260206 WA0017

Akalla ’yan jarida goma sha huɗu daga kafafen yaɗa labarai daban-daban sun jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a jihar Bauchi, yayin da suke kan aikin ɗauko labarai tare da tawagar Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC).

Hatsarin ya faru ne a titin Yashi zuwa Yelwan Duguri, a ƙaramar hukumar Alkaleri, jim kaɗan bayan ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, ya ƙaddamar da makarantar sakandare ta Gwamnati (GSS) a Yelwan Duguri.

Advertisement

Wasu Bata Gari Sun Kai Hari Hedikwatar Jam’iyyar ADC

Rahotanni sun ce tawagar na kan hanyarsu ce ta zuwa buɗe wasu ayyukan NEDC a yankin lokacin da lamarin ya faru.

Advertisement

’Yan jaridun da abin ya shafa sun fito ne daga kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da Channels TV, AIT, NTA, TVC, ARISE News, da kuma jaridun The Guardian, The Nation, da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

An kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Yelwan Duguri domin samun agajin gaggawa, kafin daga bisani a tura su zuwa Babban Asibitin Bauchi.

Advertisement

Rahotanni sun tabbatar da cewa babu asarar rai, duk da lalacewar wasu kayayyakin aikin jarida.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending