News
Jama’a Sun Hallaka Wani Wanda Ake Zargi Da Ƙwaƙule Idanun Ɗan Maƙwabcinsa A Nasarawa
Wani mummunan lamari ya faru a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa, inda jama’a suka kashe tare da ƙone gawar wani mutum da ake zargi da kashe wani yaro tare da ƙwaƙule masa idanu.
Rahotanni sun ce an gano gawar yaron ne a cikin wani rami da ke wani gida a unguwarsu, abin da ya tayar da hankalin al’umma.
’Yan banga sun kama mutumin da ake zargi, wanda ake cewa tsohon dogari ne a Fadar Sarkin Keffi. Sai dai kafin isowar ’yan sanda, fusatattun jama’a sun mamaye wurin, suka yi masa duka har lahira, sannan suka ƙone gawarsa.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:30 na rana, amma kafin isowarsu, jama’a sun riga sun kashe wanda ake zargin.
Ya ƙara da cewa jama’a sun kai wa ’yan sanda hari, inda wasu jami’an suka jikkata, tare da lalata motocinsu.
A nasa ɓangaren, Kakakin Sarkin Keffi, Yahaya Ladan Shafale, ya ce tun da dadewa aka sallami mutumin daga aikin fadar kafin faruwar lamarin.
An ɗauki gawar wanda aka kashe zuwa Babban Asibitin Gwamnati da ke Keffi, yayin da ’yan sanda ke ci gaba da bincike.
Lamarin ya haifar da fargaba a garin, inda ake kira da a bar doka ta yi aikinta tare da kauce wa ɗaukar doka a hannu.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
