News
Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf Shugaban NAHCON
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), inda ya nemi Majalisar Dattawa ta gaggauta tabbatar da naɗin.
Naɗin ya yi daidai da tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2006, kamar yadda wasiƙar da shugaban ƙasar ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ta bayyana.
Amurka Za Ta Tura Dakaru 200 Nijeriya
Rahotanni sun nuna cewa naɗin Ambasada Yusuf ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya yi a cikin wannan makon, bayan ya shafe kusan watanni 14 yana riƙe da muƙamin.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne, wanda ya taba zama Jakadan Najeriya na Musamman kuma Cikakken Wakili a Jamhuriyar Türkiye tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024.
