News
Fasinjoji 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Tangarɗar Injin Jirgin Arik Air
Fasinjoji 80 sun tsallake rijiya da baya bayan da wani jirgin kamfanin Arik Air ya fuskanci matsalar injin da ta tilasta masa karkatar da hanya domin saukar gaggawa a jihar Edo.
Jirgin mai kirar Boeing 737-700, wanda ke kan hanyarsa daga Legas zuwa Fatakwal, ya sauya hanya zuwa Filin Jirgin Sama na Benin a ranar Laraba, bayan da matukan jirgin suka ji wata ƙara mai ƙarfi daga injin gefen hagu yayin da jirgin ke shirin sauka.
Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf Shugaban NAHCON
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Arik Air ta bayyana cewa jirgin mai lamba W3-740, mai rajista 5N-MJF, na dab da sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Fatakwal da ke Omagwa ne lokacin da matsalar ta faru.
Kamfanin ya ce matukan jirgin sun yanke shawarar karkatar da jirgin zuwa Benin a matsayin matakin kariya domin tabbatar da tsaron fasinjoji da ma’aikatan jirgin.
Arik Air ta tabbatar da cewa babu wanda ya samu rauni a lamarin, inda aka sauke dukkan fasinjoji 80 lafiya. Haka kuma, an tanadi hanyoyin da za su kai su zuwa inda suka nufa na ƙarshe.
Hukumar Binciken Hatsurran Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB) ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin matsalar injin da ta taso yayin jirgin na sararin samaniya.
Hukumar ta ce za ta fitar da rahoton farko cikin kwanaki 30, yayin da cikakken rahoto zai fito bayan kammala bincike.
NSIB ta kuma buƙaci duk wanda ke da bayanan da za su taimaka wa binciken da ya tuntuɓe ta ta hanyoyin hukuma, tare da alƙawarin ci gaba da sanar da jama’a sabbin bayanai yayin da bincike ke gudana.
