Connect with us

News

Jami’an DSS Sun Kama Wanda Ya Sace Yaro Dan Shekaru 5 a Kano

Published

on

Dss

Rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar ceto wani yaro mai shekaru biyar, Muhammad Haruna, daga hannun masu garkuwa da mutane a Kauyen Danzaki, karamar hukumar Minjibir.

An gudanar da aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:40 na yamma ranar Alhamis, bayan an sami rahoton cewa an sace yaron kuma masu garkuwar suna neman miliyan goma sha biyar a matsayin kudin fansa.

Advertisement

Hisbah Ta Haramta Wa Mata Hawa Gefen Adaidaita Sahu A Kano

A yayin aikin, jami’an DSS sun cafke Aminu Mukhtar mai shekaru 20, wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne, a lokacin da yake tattaunawa da mahaifin yaron ta wayar salula don neman kudin fansa. Mukhtar ya amsa cewa shi ne ya sace yaron domin neman kuɗin fansa.

Advertisement

Hukumar DSS ta ci gaba da kira ga al’umma da su rika bayar da rahoton duk wani abu da suka lura da shi domin taimakawa wajen yakar garkuwa da yara da kuma tabbatar da tsaron su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending