News
BUƊAƊƊIYAR WASIKA: Lauya Ta Bukaci Hukumar Hisbah Ta Ƙara Wayar Da Kai Kan Tarbiyyar Yara
Wata lauya mazauniyar Kano, Hajiya Bilkisu Ibrahim Suleiman, ta rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Hukumar Hisbah, inda ta buƙaci hukumar ta ƙara himma wajen wayar da kai kan tarbiyya da kyawawan dabi’u, biyo bayan cece-ku-cen da wani gagarumin bikin zagayowar ranar haihuwa da aka shirya wa kananan yara uku ya jawo a cikin al’umma.
A wasiƙar mai taken “Kare Darajojin Tarbiyya da Kiyaye Hankalin Matasa Masu Tasowa,” Bilkisu ta bayyana damuwa kan yadda ake ƙara nuna alfarma fiye da kima, musamman a al’amuran da suka shafi yara ƙanana.
Jami’an DSS Sun Kama Wanda Ya Sace Yaro Dan Shekaru 5 a Kano
Ta ce muhawarar da bikin ya haifar ba wai kan girman shagalin ba ne kawai, illa tasirin zamantakewa da tarbiyya da irin waɗannan abubuwa ke haifarwa — musamman a lokacin da iyalai da dama ke fama da matsin tattalin arziki da kuma matsalolin tsaro.
A cewarta, yarinta mataki ne mai matuƙar muhimmanci wajen gina halaye da fahimtar rayuwa. Don haka, nuna alfarma ga yara tun suna kanana na iya sa su rungumi son abin duniya fiye da kima, abin da ka iya rage darajar halaye irin su tawali’u, godiya da gamsuwa.
Ta jaddada cewa muhimmin abin dubawa ba wai yin biki ba ne, sai dai irin darussan da ake koyawa yara masu saurin kwaikwayo, da kuma matsin lambar da irin waɗannan bukukuwa za su iya haifarwa a tsakanin takwarorinsu.
Har ila yau, ta gargadi cewa saba da bukukuwa masu tsada ga kananan yara na iya sauya dabi’un al’umma a hankali, tare da haifar da buri da wasu yara ba za su iya cimmawa ba saboda halin tattalin arzikin iyalansu.
Lauyar ta buƙaci Hisbah ta ƙara mayar da hankali kan wayar da kai da ilmantarwa mai ma’ana kan tarbiyya, maimakon tsauraran matakai kawai. Ta kuma yi kira ga iyaye su zama abin koyi wajen sauƙin kai da kulawa da jin daɗin jama’a, tare da fifita halayya da tarbiyya a kan nuna alfarma.
A ƙarshe, ta bayyana cewa manufar wasiƙar ba don kunyata ko zargin kowa ba ce, sai dai domin kare tubalin tarbiyyar yara da makomar al’umma gaba ɗaya, tana mai cewa martani mai hikima daga Hisbah zai ƙarfafa gwiwar jama’a tare da nuna jagoranci mai tausayi da kishin al’umma.
