Connect with us

News

Gobara Ta Lalata Shaguna Sama Da 1,500 A Kasuwar Singer Dake Kano ‎

Published

on

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.37 768x385

Wata babbar gobara da ta tashi a Kasuwar Singer da ke birnin Kano ta lalata shaguna da kwantena sama da 1,500, tare da haddasa asarar dukiyoyi da aka kiyasta sun haura Naira biliyan 5.

Shugaban ƙungiyar ci gaban kasuwar, Junaid Zakari, ya bayyana cewa yankin da gobarar ta fi kamawa na ɗaya daga cikin wuraren kasuwar da suka fi cunkoso da kayayyaki masu daraja.

Advertisement

BUƊAƊƊIYAR WASIKA: Lauya Ta Bukaci Hukumar Hisbah  Ta Ƙara Wayar Da Kai Kan Tarbiyyar Yara

Da yake zantawa da SolaceBase, ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar ta cinye rumfuna da kwantena na ’yan kasuwa da dama, ciki har da ƙananan ’yan kasuwa da ke rayuwa da abin da sana’arsu ta samar a kullum.

Advertisement

A cewarsa, asarar ta yi matuƙar girma, musamman ga waɗanda ke gudanar da kasuwanci da jarin aro ko tallafin ƙungiyoyi, lamarin da ka iya jefa su cikin mawuyacin hali na tattalin arziƙi.

Wasu ’yan kasuwar sun ce sun yi asarar kayayyaki da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyin naira, yayin da wasu kuma suka bayyana cewa duk kuɗaɗen da ke shagunan su sun ƙone gaba ɗaya.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan wutar, sai dai har yanzu suna ci gaba da aikin sanyaya wasu wurare domin hana sake tashinta.

Lokacin da aka kai ziyara kasuwar da safe, an ga hayaki na tashi daga wasu sassa, yayin da ’yan kasuwa ke laluben tarkacen kayayyaki domin ceto abin da ya rage.

Advertisement

Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne da yammacin ranar Asabar, ta kuma ci gaba da ƙonewa har cikin daren Lahadi, lamarin da ya haddasa fargaba da tashin hankali a tsakanin ’yan kasuwa.

Haka kuma, an ruwaito cewa wannan gobara ta biyo bayan wata makamanciyar wadda ta faru a kasuwar a baya-bayan nan.

Advertisement

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana musabbabin tashin gobarar ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending