Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Kaduna

Published

on

Aƙalla mutum biyar da ake zargin masu safarar makamai ne aka kama su, tare da ƙwato kusan bindigogi 30 a yayin wasu hare-haren tsaro da aka gudanar a sassa daban-daban na Jihar Kaduna.

Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta ce hare-haren sun kuma yi sanadiyyar kashe wasu da ake zargin Ƴan bindiga ne yayin artabu da jami’an tsaro.

Advertisement

Mutum 4 Sun Mutu, 18 Sun Jikkata A Turmutsitsin Karbar Sadakar Ramadan A Katsina

Kwamishinan Ƴansanda, Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya zayyano manyan nasarorin da rundunar ta samu cikin makonni biyu da suka gabata.

Advertisement

Muhammad ya ce hare-haren na daga cikin matakan da ake ci gaba da ɗauka bisa sahihan bayanan sirri domin kai farmaki kan sansanonin Ƴan bindiga da maɓoyarsu a ƙananan hukumomin Kajuru, Tafa, Igabi da Kauru.

A cewarsa, an tarwatsa sansanoni da dama bayan musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da Ƴan ta’adda, lamarin da ya kai ga hallaka wasu daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi.

Advertisement

“Sakamakon waɗannan hare-hare, an kama wasu fitattun Ƴan bindiga da ake nema ruwa a jallo, sannan an cafke masu safarar makamai guda biyar. Haka kuma, an ƙwato tarin makamai da alburusai,” in ji Kwamishinan.

Ya ce kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi kirar AK-47 guda uku na waje, bindigogi 21 da aka ƙera a gida, bindiga kirar SMG guda ɗaya, bindigogin hannu guda biyu na waje da kuma guda huɗu da aka ƙera a gida.

Advertisement

Ya ƙara da cewa an kuma ƙwace tarin miyagun ƙwayoyi da ake zargin an samar wa miyagun laifuka a yayin samamen.

A wani ci gaba mai alaƙa da haka, rundunar Ƴansanda ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun kama wani Adamu Aminu na garin Jaji a Ƙaramar Hukumar Igabi ranar 20 ga Fabrairu da misalin ƙarfe 9 na dare.

Advertisement

Kwamishinan Ƴansanda, Rabiu Muhammad, ya ce an samu wanda ake zargin da bindigogi ƙirar AK-47 guda shida da aka ƙera a gida, bindigogin reɓolɓer guda uku da aka ƙera a gida, bindigogin hannu guda biyu da aka ƙera a gida da kuma alburusai (magazines) na AK-47 guda bakwai na waje.

“An kuma ƙwato baƙin takalmin soja ƙirar Wellco guda ɗaya daga hannunsa. Binciken farko ya nuna cewa yana da hannu a sana’ar ƙera da safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke ƙara rura wutar ayyukan laifi a ciki da wajen Kaduna State,” in ji shi.

Advertisement

Kwamishinan ya ƙara da cewa an kama wani da ake zargi, Abubakar Hassan na Unguwar Rogo a Ƙaramar Hukumar Jos North ta Jihar Filato, dangane da lamarin.

Muhammad ya ce bincike na ci gaba domin tarwatsa wannan ƙungiya, gano hanyoyin rarraba makaman da aka ƙwato da kuma tabbatar da cewa an hukunta duk masu hannu a ciki.

Advertisement

Hakazalika, Ƴansanda sun kama wasu mutum uku a Kasuwan Magani ranar 17 ga Fabrairu bisa zargin mu’amalar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Waɗanda ake zargin, Peter Pama da Saleh Monday duk na Iburu, da kuma Sunday Makama na Kasuwan Magani, an ce an same su da bindiga kirar AK-47 da aka ƙera a gida da kuma bindiga kirar pump-action.

Advertisement

“Waɗannan nasarori suna nuna jajircewarmu wajen aiwatar da aikin Ƴansanda bisa sahihan bayanan sirri da kuma ƙudurinmu na katse hanyoyin samar da makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke rura wutar laifuka a jihar,” in ji Muhammad.

Ya sake jaddada cewa Rundunar Ƴansandan Kaduna State ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifi, tare da yaba wa Sufeto Janar na Ƴansanda, Kayode Egbetokun, kan jagoranci da dabarun da yake bayarwa.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending