News
Shugaba Tinubu Ya Tura Sabbin Jakadu 65 Zuwa Ƙasashe Daban-daban
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura jakadu da manyan kwamishinoni 65 domin wakiltar Nijeriya a ƙasashe daban-daban da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sanarwar ta fito ne daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga.
Wani Ya Kashe Ɗan Uwansa Saboda Ya Harbe Shi A Mafarki
Ya ce daga cikin jakadun akwai 34 ‘yan siyasa da aka naɗa, yayin da 31 kuma ƙwararrun jami’an diflomasiyya ne.
Daga cikin fitattun waɗanda aka naɗa akwai tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode wanda aka tura zuwa Jamus, da mai taimaka wa shugaban ƙasa Reno Omokri wanda zai wakilci Najeriya a Mexico.
Haka kuma akwai tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida Abdulrahman Dambazau wanda zai je China, yayin da Sanata Jimoh Ibrahim zai wakilci Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Abia Okezie Ikpeazu da aka tura zuwa Spain, da tsohon Ministan Lafiya Isaac Adewole wanda zai yi aiki a Canada.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da sunayen jakadun a watan Disamban shekarar 2025, kuma ana sa ran za su fara aiki bayan sun kammala horo da kuma samun amincewar ƙasashen da za su wakilta Nijeriya a cikinsu.
