News
Dakarun Soji Sun Samu Nasarar Kashe Ƴanta’adda 45 A Katsina
Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 45 a wani kazamin bata-kashi da suka yi a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Sai dai a fafatawar da sojojin suka kai, an samu hasarar rayuka, yayin da wani jami’in soji, Kyaftin Paul Hassan, da wasu sojoji biyu suka mutu a yayin arangamar da suka yi.
Rikicin ya faru ne a ranar 6 ga Maris, 2026, lokacin da sojojin da ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta Forward Operating Base (FOB) da ke Dan Ali suka yi taho-mu-gama da ‘yan bindiga dake dauke da muggan makamai wadanda aka ce sun nufi karamar hukumar Musawa ne.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasir Mua’zu ya fitar a ranar Asabar, ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Alhazawa da ke karamar hukumar Musawa a ranar 5 ga watan Maris, inda suka yi yunkurin yin satar shanu ba tare da samun nasara ba.
A cewarsa, al’ummar yankin tare da goyon bayan wasu tubabbun ‘yan bindiga a yankin, sun bijirewa harin, inda suka kashe hudu daga cikin maharan tare da kwato shanun da suka sace.
Ya kuma ƙara da cewa daga baya ‘yan fashin suka sake haduwa suka sake dawowa washegari a wani mataki na daukar fansa.
Mua’zu ya ce yayin da suke zuwa Musawa ta unguwar Maidabino A, maharan sun ci karo da sojojin da aka girke a barikin sojoji na gaba da ke Dan Ali.
Inda sukayi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin halaka ‘yan bindiga 45 a tare da waɗanda suka jikkata da dama.
Ya bayyana cewa, wani mai suna Alti, ƙane kuma na biyu a cikin mayaƙan fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Adamu Alieru, da wani babban dan bindiga mai suna Damale, na daga cikin wadanda aka kashe a fafatawar.
Kwamishinan ya yaba da jarumtaka da sadaukarwar da sojojin da abin ya shafa suka yi, inda ya bayyana ayyukansu a matsayin cikakkiyar jarumtaka wajen kare al’umma daga kungiyoyin marasa tsoron Allah.
Ya kara da cewa nasarar da aka samu ya haifar da cikas ga ayyukan ‘yan bindiga a yankin tare da ceto rayuka da dama.
Mua’zu ya kuma mika ta’aziyyar gwamnatin jihar Katsina ga iyalan sojojin da aka kashe, tare da amincewa da sadaukarwar da suka yi wajen yaki da ‘yan bindiga masu satar mutane da shanun da kuma kashe al’uma.
Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da bibiyar kungiyoyin masu dauke da makamai da ke haddasa tashe-tashe hankula a jihar har sai an samu kwanciyar hankali.
