News
Iran Ta Kai Hare-hare Da Makamai Masu linzami Kan Birane Da Dama Na Isra’ila
Iran ta sake kai hare-hare sassan Isra’ila ta hanyar amfani da makamai masu linzami waɗanda a wannan karon ta yi ruwansu lokaci guda a yankunan kudanci da arewacin ƙasar.
Kafin yanzu Iran na kai hare-hare ne daban daban ko dai a yankin Arewacin Isra’ilar ko kuma kudanci saɓanin wanda aka gani a yau Litinin dai dai lokacin da ake shiga kwana na 9 da faro yaƙin ƙasashen.
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Garin Maƙarfi A Jihar Kaduna
An ji ƙarar kuwwar ankararwa a birane da dama na Isra’ilar tun daga Haifa har zuwa Dimona.
Duk da cewa Isra’ila ta yi nasarar tare wasu daga cikin makaman masu linzami amma bayanai sun ce hare-haren na Iran sun yi gagarumar ɓarna.
Bayanai sun ce hare-haren sun shafi yankunan Tel Arad da Dimona waɗanda ke gaba da Negev, wato yankin da cibiyar binciken makaman nukiliya na ƙasar ya ke.
Haka zalika an ji kuwwar ankararwa a Tiberias da tsaunukan Jezreel kana Beisan da kuma kwarin Galilee.
Bayanan da Isra’ila ta fitar ta ce ta sanya kuwwar ne don ankarar da jama’arta amma ba don hare-haren na Iran sun yi mata illa ba.
Mazauna yankunan da Iran ta harba makaman dai sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe sai dai babu tabbacin ko ƙarar daga tare makamin ne ko kuma daga saukar shi.
