News
SERAP Ta Kai Gwamnatin Tarayya Ƙara Kotu
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama da yaki da cin hanci ta SERAP ta shigar da kara a kotun ECOWAS Community Court of Justice da ke Abuja, tana kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kin janye wata doka da take bai wa jami’an tsaro damar sauraren wayoyin jama’a.
Kungiyar ta ce dokar da aka fi sani da ka’idojin sa ido kan hanyoyin sadarwa ta shekarar 2019 tana bai wa kamfanonin sadarwa umarnin girka na’urori da jami’an tsaro za su rika amfani da su wajen sauraren kira, sakonni, bayanan intanet da sauran mu’amalar sadarwar mutane, da sunan kare tsaron kasa da kuma yaki da laifuka.
Ayyuka Takwas Masu Tarin Lada A Kwanaki 10 Na Ƙarshen Watan Ramadan.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya fitar, ya bayyana cewa kungiyar ta dauki matakin zuwa kotu ne bayan zargin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa an saurari tattaunawar wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Rahotanni sun ce El-Rufai ya yi ikirarin cewa an saurari kiran wayar Ribadu, inda aka ji yana cewa a kama shi.
Kungiyar SERAP ta roki kotun ta bayyana cewa kin janye dokar sa ido kan hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi ya saba wa doka, kuma yana take hakkin jama’a na sirrin rayuwa da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki.
Haka kuma kungiyar ta bukaci kotun ta umarci gwamnatin Najeriya ta janye dokar nan take, sannan ta fara samar da sabuwar doka da za ta dace da yarjejeniyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.
Lauyoyin kungiyar sun bayyana cewa dokar ta bai wa jami’an gwamnati iko mai yawa na sauraron wayoyin jama’a ba tare da cikakken sa ido na kotu ba, abin da ka iya haifar da amfani da ita wajen takura wa ‘yan siyasa masu adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula da masu sa ido kan zabe.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa cewa wannan lamari na iya zama barazana ga sahihancin zaben shekarar 2027, domin idan jama’a suka ji ana iya sauraron tattaunawarsu, hakan na iya hana su tattauna harkokin siyasa cikin ‘yanci.
SERAP ta kara da cewa duk wani takaita hakkin sirri dole ne ya kasance bisa doka, ya zama dole kuma ya dace da dalilin da aka kawo, amma ta ce wannan doka ba ta cika wadannan sharudda ba.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa dokar tana dauke da sabani,
domin wasu sashe na takaita ikon sauraron waya ga mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro da kuma hukumar tsaro ta farin kaya, amma wani sashe kuma ya fadada ikon ga wasu hukumomi kamar ‘yan sanda, hukumar leken asiri ta kasa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi.
SERAP ta ce wannan rashin bayyananniyar hanya na iya haifar da amfani da dokar ba bisa ka’ida ba.
Kungiyar ta jaddada cewa gwamnati na da hakkin kare tsaron kasa da yaki da manyan laifuka, amma dole ne hakan ya kasance cikin iyakar doka da kuma girmama hakkin dan Adam.
