News
Iran Ta Gindaya Sharudda 3 Domin Kawo Ƙarshen Yaƙi
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana sharudda uku da ƙasar Iran ta gindaya domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Amurka da kuma Isra’ila.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ɗaya daga cikin manyan sharuddan shi ne Amurka ta biya diyya kan barnar da hare-haren ta suka jawo a Iran.
Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Nauyin Horar Da Marubuta Labaran Wassanni 10
Ya ce ya bayyana waɗannan sharuddan ne yayin ganawarsa da shugabannin Russia da Pakistan, ƙasashen da suka soki Amurka da Isra’ila kan fara yaƙin.
“A tattaunawa ta da shugabannin Rasha da Pakistan, na sake jaddada kudurin Iran na samar da zaman lafiya a yankin. Hanya guda da za a kawo ƙarshen wannan yaƙi — wanda gwamnatin sahyoniyawa da Amurka suka tayar — ita ce a amince da haƙƙin Iran na halal, a biya diyya, sannan a samar da tabbatattun garantin ƙasa da ƙasa domin hana irin wannan hari a gaba,” in ji shi.
Yadda rikicin ya ƙara tsananta
Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 1,300 ne suka mutu a Iran tun bayan fara yaƙin kwanaki 12 da suka wuce, lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan ƙasar.
A martanin Iran kuwa, hare-haren ramuwar gayya sun kashe sojojin Amurka takwas, tare da mutuwar aƙalla mutane 12 a Isra’ila.
Daga cikin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren Amurka da Isra’ila har da tsohon jagoran addini na Iran Ali Khamenei, da kuma sama da ’yan makaranta mata 160 da suka mutu bayan makami mai linzami ya faɗa makarantar su.
Wani binciken sojojin Amurka ya tabbatar da cewa harin da ya afkawa makarantar na daga cikin hare-haren da Amurka ta kai, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito a ranar Laraba.
Har yanzu ana ci gaba da musayar hare-hare
Duk da ikirarin Amurka cewa ta lalata mafi yawan ƙarfin sojin sama da na ruwa na Iran tare da yawancin makaman linzami, Iran na ci gaba da harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi zuwa Isra’ila da kuma wuraren da Amurka ke da muradi a Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma, Iran ta rufe mashigar Strait of Hormuz, inda kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya ke ratsa wa. Matakin ya janyo hauhawar farashin mai a kasashen duniya, ciki har da Najeriya.
