Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 56, Ta Tarwatsa Wuraren Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano 

Published

on

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta sanar da kama mutane 56 tare da tarwatsa wurare da dama da ake zargin ana sayar da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

Mai magana da yawun hukumar a Kano, ASN Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Advertisement

Ministan Tsaron Ya Gayyaci Shugabannin Rundunonin Soji Kan Karuwar Hare-hare A Arewa

Ya ce kamen ya biyo bayan wani samame na kwanaki uku da jami’an hukumar suka gudanar a wasu sassa na jihar, a wani mataki na ƙarfafa yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

A cewarsa, Kwamandan NDLEA na jihar Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ƙarƙashin wani shiri mai suna “Operation Ramadan Mubarak”, domin rage yawaitar miyagun ƙwayoyi a lokacin watan Ramadan da ma bayan watan.

Sanarwar ta ce tsakanin 6 zuwa 8 ga Fabrairu, jami’an NDLEA sun kai samame wuraren da aka dade ana zargin ana sayar da miyagun ƙwayoyi a unguwannin Kofar Mata, Fagge, Kasuwar Rimi, Medile, Badawa da Sabon Gari a cikin birnin Kano.

Advertisement

Haka kuma, samamen ya bazu zuwa wasu wurare a cikin birnin da ma wajen birnin Kano, inda jami’an suka rusa cibiyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba.

NDLEA ta ce a yayin samamen jami’anta sun kwato miyagun ƙwayoyi iri-iri, ciki har da wiwi (cannabis sativa), Exol-5, diazepam da pregabalin, da sauran ƙwayoyi da aka haramta.

Advertisement

A cewar kwamandan, wannan kamen ya zama wani babban mataki a yaƙin da hukumar ke yi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.

Sanarwar ta kuma ce ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Yunusa Yasin mai shekaru 30 daga Badawa, ana zarginsa da hannu a wani kisan kai da ya faru kimanin shekaru biyar da suka gabata.

Advertisement

NDLEA ta ce an miƙa wanda ake zargin ga rundunar ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a.

Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi domin taimakawa wajen kare lafiyar jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending