Connect with us

News

Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano

Published

on

15th and 14th Emir of Kano

 

Kotun Ƙoli na shirin yanke hukunci kan rikicin shari’ar da ya dabaibaye Masarautar Kano.

Advertisement

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da suka taso daga sauye-sauyen da aka yi wa tsarin masarautar, wanda ya haifar da mayar da wasu sarakuna kan muƙamansu da kuma sake amincewa da su a matsayin sarakuna.

Iran Ta Gindaya Sharudda 3 Domin Kawo Ƙarshen Yaƙi

Advertisement

Majiyoyi da ke da masaniya kan yadda shari’ar ke gudana sun shaida wa jaridar Kano Times cewa, hukuncin da kotun za ta yanke zai tantance ko sauye-sauyen da aka yi wa masarautar sun halatta a doka, tare da fayyace ikon da Gwamnatin Jihar Kano ke da shi kan harkokin sarautun na gargajiya.

Wata majiya da ke kusa da shari’ar ta shaida wa jaridar cewa, ana sa ran kotun za ta yanke hukuncin a wannan watan, duk da cewa ba a bayyana takamaiman ranar ba.

Advertisement

Majiyar ta ce: “Abin da zan iya faɗa shi ne, Kotun Koli za ta yanke hukunci a wannan watan na Maris. Ba zan iya faɗin ainihin ranar ba, amma tabbas za a yanke hukuncin a watan Maris.

 

Advertisement

 

LEADSHIP HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending