News
Sifaniya Ta Janye Jakadiyarta Daga Isra’ila
Ƙasar Spain ta sanar da sallami jakadiyarta a Isra’ila, Ana Salomon, wacce ta rike mukamin tun watan Yuli na 2021. Wannan na zuwa ne bayan watanni da aka kira ta zuwa Madrid sakamakon tsamin dangantaka da gwamnatin Isra’ila.
An amince da matakin ne a Majalisar Ministocin Spain bisa shawarar Ministan Harkokin Waje Jose Manuel Albares, kuma an wallafa shi a jaridar gwamnati a ranar 11 ga Maris.
Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano
Dangantakar kasashen biyu ta kara tsami ne bayan Spain ta zargi Isra’ila da yin “zarge-zarge marasa tushe” da kuma daukar “matakai da ba za a amince da su ba” kan ministocin Spain Yolanda Diaz da Sira Rego, bayan sukar da Madrid ta yi kan matakan Isra’ila a Zirin Gaza da kuma matakan da Firaministan Spain Pedro Sanchez ya sanar bayan hare-haren Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
Bayan sallamar jakadiyar, ofishin jakadancin Spain a Isra’ila zai kasance karkashin jagorancin jami’in wucin gadi har sai an nada sabon jakada. Har yanzu dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ba ta daidaita ba, yayin da Isra’ila ma ba ta da jakada a Spain tun bayan da jakadanta ya bar kasar a 2024 bayan Spain ta amince da Kasar Falasdinu.
