Connect with us

News

Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Takaita Zirga-zirga Da Ta Sa A Jos

Published

on

filato

Gwamnatin Jihar Filato ta sassauta dokar hana fita na awanni 48 da ta kafa a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, bayan mummunan harin da aka kai wa mazauna Angwan Rukuba a ranar Lahadi da ta gabata.

A ranar Talata Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta sanar cewa an sassauta dokar daga karfe 7 na safe zuwa 3 na rana.

Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Fashi 4 Hukuncin Shekaru 10 a Gidan Yari A Kano 

“Daga ranar 1 ga Afrilu, 2026, an sassauta dokar hana fita za ta fara aiki ne daga karfe 3 na rana zuwa ƙarfe 7 na safe. Ana ba da izini ga mazauna su gudanar da harkokinsu na halal a cikin sa’o’i da aka sassauta dokar,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa gwamnati na kira ga jama’a da su ci gaba da zama cikin natsuwa, su kasance masu lura da bin doka, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sa ido don tabbatar da zaman lafiya da tsari.

Kwamishinar ta gode wa jama’a bisa juriya da haɗin kai da suka nuna a wannan lokaci, tare da jaddada kudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending