Connect with us

News

Gwamnatin Sokoto Ta Samu Yabo Kan Tallafa wa Marayu da Mabukata

Published

on

IMG 20260331 WA0011

Daga Mukhtar A. Haliru, Tambuwal

 

An yaba wa Gwamnatin Jihar Sokoto bisa kokarin da take yi wajen tallafa wa marayu da sauran mabukata a fadin jihar.

Yabon ya fito ne daga Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal kuma Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jihar Sokoto (ALGON), Hon. Abba Shehu Tambuwal, yayin kaddamar da rabon kayan tallafin Sallah da gwamnatin jihar ta samar.

Auren Bazawara Da Budurwa: Muhawara Kan Zabi Da Fahimta ‎

Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna, Dakta Ahmad Aliyu Sokoto, ta raba tallafin ne ga dukkan kananan hukumomi ta hannun Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar, wadda Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ke jagoranta, tare da kulawar ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa.

Advertisement

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa, ya zama wajibi a yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa wajen gudanar da irin wannan aiki duk da yawan bukatun da ke gabansa.

> “Dole ne mu yaba wa Mai Girma Gwamna bisa dagewarsa wajen gudanar da wannan aiki, duk da dimbin ayyukan da ke gabansa,” in ji shi.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin rabon tallafin a Karamar Hukumar Tambuwal, wanda kuma shi ne Kwamishinan Kudi na Jihar Sokoto, Hon. Muhammad Jabbi Shagari (Ubandoman Shagari), ya bayyana yadda aka tsara rabon kayan.

Ya ce dukkan gundumomin da ke cikin karamar hukumar za su amfana da tallafin, inda yara marayu maza da mata za su samu shadda ko atamfa guda biyar tare da kudi naira dubu goma.

Haka kuma, uwayen marayu da sauran mabukata za su karbi buhunan shinkafa mai nauyin kilo 25 tare da kudi naira dubu goma domin taimaka musu yayin bukukuwan Sallah.

Taron ya samu halartar wakilin Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Tambuwal, Alhaji Umar Sarkin Dutsi, da wakilin Sadaukin Sakkwato, wanda Mukhtar A. Haliru ya wakilta, tare da mambobin kwamitin da wasu daraktocin karamar hukumar..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending