News
Har Yanzu Kuɗin Kashewa Na Ɗalibai Na Wata-Wata N20,000 Ne Ba N25,000 —NELFUND
Hukumar ba da lamunin karatu ta ƙasa (NELFUND) ta ce kuɗin sa wa a aljihu na ɗalibai da take ba su duk wata yana nan a kan Naira 20,000.
Hukumar ta yi wannan ƙarin hanske a cikin jawabin da ta fitar a ranar Litinin a Abuja ta hannun daraktar sadarwa, Oseyemi Oluwatuyi.
Shugaba Tinubu Na Son Majalisar Dokoki Ta Amince A Kara Naira Tiriliyan 9 A Kasafin Kudin 2026
Mrs Oluwatuyi ta ce, yin bayanin ya zama dole soboda labarin ƙarya da ake yaɗawa a dandalin sada zumunta da ke nuna cewa ta ƙara kuɗin wata-wata da take bai wa ɗaliban zuwa Naira 25,000.
Ta shawarci ɗalibai da su yi watsi da rahotannin tare da bibiyar hanyoyin sadarwa na hukumar.
A cewarta, kuɗin da hukumar ta amince domin bai wa ɗalibai shi ne Naira 20,000.
Mrs Oluwatuyi ta jaddada aniyar NELFUND ta yin komai a buɗe da ci gaba da tallafa wa ɗalibai a faɗin ƙasar nan.
Ta kuma gode wa ɗaliban bisa haɗin kan da suke ba ta inda ta buƙace su a kodayaushe su riƙa neman sahihan labarai daga hukumar.
Daraktar ta ce ɗalibai za su iya tura saƙon neman taimako ko ƙarin haske ta hanyar imel da shafukanta na sada zumunta.
Ta ƙara da cewa NELFUND za ta ci gaba da fitar da bayanan kan duk abubuwan da ke faruwa a kan lokaci domin tabbatar da ɗaliban na samun sahihan labarai.
