News
Ministoci 3 Cikin 50 Ne Kaɗai Su Ka Yi Murabus Don Takara A Zaɓen 2027
Yayin da wa’adin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya baiwa masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa suyi murabus idan har suna son tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2027 ya ƙare, ministoci 3 cikin fiye da 40 da ake dasu ne kaɗai su ka yi murabus.
Matakin wadda ke ƙunshe cikin dokar zaɓe ta 2026 da aka yiwa gyaran fuska, ta buƙaci dukkan wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati a matakin tarayya da jihohi da suka haɗa da ministoci da kwamishinoni, da masu bada shawara, da shugabannin hukumomi da ma’aikatu su ajjiye muƙamansu gabanin duk wani babban zaɓe a Najeriya, idan har sun yanke shawarar tsayawa takara.
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 3 Da 6 Ga Afrilu A Matsayin Rana Kun Hutu
Ya zuwa ƙarewar wa’adin da shugaba Tinubu ya bayar a jiya Talata, ministocin Najeriya 3 da suka haɗa da na harkokin waje Yusuf Maitama Tuggar da na sufuri Saidu Alkali da kuma ƙaramin ministan ma’aikatar kula da ayyukan jinƙai Yusuf Sununu ne kaɗai su ka yi murabus.
Rahotanni sun ce Tuggar ya yi murabus ɗin ne don neman kujerar gwamnan Bauchi a zaɓen dake tafe, yayin da Alkali ke son maye gurbin gwamna Inuwa Yahya a shugabancin jihar Gombe, sai kuma Sununu da ake sa ran zai tsaya takarar neman kujerar sanata a Kebbi.
Baya ga ministocin, wasu muƙarraban gwamnatin Tinubu sun sanar da murabus ɗinsu, cikinsu akwai babban mai taimawa shugaban, Malam Nasir Ja’oji dake neman kujerar ɗan majalisar Tarauni a Kano, sai Abdulrazak Namdas da ke zama mamba a kwamitin gudanarwar hukumar kula da yankin Neja Delta.
Akwai kuma Nasiru Yusuf Gawuna da ya ajje muƙaminsa na shugabancin kwamitin gudanarwar bankin samar da muhalli na Mortgage, tare da sanar da ficewa daga jam’iyyar APC zuwa ADC.
Duk da cewa wa’adin murabus da shugaba Tinubu ya bai wa muƙarraban nasa ya kawo ƙarshe, amma rahotanni sun ce akwai jami’an gwamnatin da dama da ke tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan takarar da suke son tsayawa a zaɓen 2027, duk da cewa suna ci gaba da riƙe muƙamansu.
