Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 3 Da 6 Ga Afrilu A Matsayin Rana Kun Hutu

Published

on

Tinubu Bola 750x430

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa Juma’a, 3 ga Afrilu Good Friday, da Litinin, 6 ga Afrilu Easter Monday,a matsayin ranakun hutu domin bikin Good Friday da Easter Monday. Wannan sanarwa ta fito ne daga ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya jaddada muhimmancin sadaukarwa da ƙauna da Yesu Almasihu ya nuna wajen ceto ɗan Adam.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani, ta fitar, Ministan ya buƙaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a ƙasa. Ya kuma bayyana ƙudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen aiwatar da shirin “Renewed Hope Agenda” domin ci gaban ƙasa.

Advertisement

DSS Sun Cafke Wata Matashiya Mai Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Harsashai A Kano

Tunji-Ojo ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu nuna ƙauna da kyautatawa ga makwabtansu ta hanyar ayyukan alheri da jin ƙai. Ya yi fatan bukukuwan Easter za su kawo sabuwar fata da ƙarfafa imani a zukatan ‘yan Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending