Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Sun Kama Mata Biyu Bisa Zargin Sace Jariri A Nasarawa ‎

Published

on

FB IMG 1775231409632

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta sanar da ceto wani jariri namiji mai kwanaki uku da aka sace a yankin Mararaba, yayin da ta kama mata biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

Mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel, ya ce mahaifiyar jaririn, Aisha Bada, mai shekaru 19, ce ta kai rahoton sace jaririn bayan wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun shiga inda take tare da jaririn suka dauke shi.

Advertisement

An Tura Ƙarin Dakarun Soji 850 Domin Tabbatar Da Tsaro A Filato

‎‘Yan sanda sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Maris, a wani gini da ba a kammala ba da ke unguwar Unguwan Bako a Mararaba, cikin karamar hukumar Karu, inda mahaifiyar ke barci tare da jaririn.

Advertisement

‎Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shetima Mohammed, ya umarci a fara bincike cikin gaggawa. Daga bisani, jami’an tsaro sun gudanar da samame bisa sahihan bayanan sirri, wanda ya kai ga kama wasu mata biyu, Furera Abdulrahman da Sadiya Abdullahi.

‎A cewar ‘yan sanda, matan sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, tare da bayyana cewa suna da wani abokin aikata laifin da har yanzu ake naima , inda ake ci gaba da kokarin cafke shi.

Advertisement

‎An kai jaririn asibiti domin duba lafiyarsa, inda aka tabbatar yana cikin koshin lafiya kafin a mika shi ga iyayensa.

 

Advertisement

 

DAILY REPORTS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending