Connect with us

News

An Kama Malamai 7 Kan Satar Amsa A Yayin Zana Jarrabawar Kwarewar Aiki A Jigawa

Published

on

JIGAWA 3 768x432 (1)

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kama wasu malamai bakwai bisa zargin aikata magudin jarrabawa yayin wata jarrabawar tantance ƙwarewar malamai da aka gudanar a fadin jihar.

Mahukunta sun ce jarrabawar, wadda Hukumar Ilimi ta Firamare ta jihar (SUBEB) ta shirya, ta haɗa da sama da malamai 8,400, kuma na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta ilimi da tabbatar da gaskiya a makarantun gwamnati.

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu Bayan Wani Rikici Kan Sayen Garin Kwaki Da Ruwan Leda A Katsina ‎

Shugaban hukumar, Haruna Musa, ya bayyana cewa an mika waɗanda ake zargi ga rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Ya ce jarrabawar, wadda ake kira Teacher Training Needs Assessment, an ƙaddamar da ita ne domin gano gibin ilimi da ƙwarewar malamai, tare da tsara horo na musamman da zai taimaka wajen inganta aikinsu.

“Ba wai kawai gwajin sani ba ne, wannan mataki na nufin dawo da kima da ƙwarewa a harkar koyarwa,” in ji shi.

Advertisement

Haruna Musa ya ƙara da cewa wannan babban tantancewa na nuna aniyar gwamnati wajen magance matsalolin da ke haifar da raguwar ingancin ilimi, tare da tabbatar da cewa ƙwararrun malamai ne kaɗai za su ci gaba da koyarwa.

Ya kuma yi gargadin cewa duk wani nau’in magudin jarrabawa, ko daga ɗalibai ko malamai, ba za a lamunce da shi ba, domin yana lalata amincin tsarin ilimi.

Haka zalika, ya gargaɗi malamai da su guji halartar aiki ba tare da izini ba, da kuma tsunduma cikin harkokin siyasa a lokacin aiki.

Hukumar ta ce kama malamai bakwai ya zama izina ga sauran, yayin da take jaddada ƙudirin ta na tabbatar da ladabtarwa da kyawawan ɗabi’u a fannin ilimi a jihar Jigawa.

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending