Connect with us

News

Ƴan Siyasa Na Sauya Sheƙa Don Biyan Buƙatun Kai, Ba Don Jama’a Ba — Muhammad Bello Zaki

Published

on

s2.reutersmedia.net 39

Fitaccen ɗan jarida, Muhammad Bello Zaki, ya bayyana cewa yawaitar sauya sheƙar da ‘yan siyasa ke yi a Najeriya ba ta da alaƙa da muradin al’umma, sai dai don cimma burinsu na kashin kai.

Zaki ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da Muhasa TV /Radio, inda ya ce sau da dama ‘yan siyasa na sauya jam’iyya ne domin samun wata dama ta siyasa ko kariya ga muradunsu, ba wai saboda wata sabuwar manufa da za ta amfani jama’a ba.

Advertisement

Gwamnatin Bauchi Ta Rufe Kasuwannin Shanu 25 A Faɗin Jihar 

A cewarsa, “Sauya jam’iyya da ake gani a yau ba don ci gaban al’umma ake yi ba. Yawanci ana yin sa ne domin anfani na kashin kai ko samun wata dama a siyasa.”

Advertisement

Ya kara da cewa irin wannan dabi’a na haifar da koma baya ga tsarin dimokuraɗiyya, domin yana rage amincewar da jama’a ke yi wa shugabanni da kuma jam’iyyun siyasa.

Haka kuma, ya bukaci al’umma da su rika sanya ido kan ‘yan siyasa tare da rike su da alhakin abin da suka dauka wa kansu, musamman wajen cika alkawuran da suka yi kafin samun mulki.

Advertisement

Zaki ya jaddada muhimmancin samar da tsauraran dokoki da za su rage yawaitar sauya sheƙa ba tare da hujja mai karfi ba, domin kare mutuncin tsarin siyasa da inganta shugabanci nagari a ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending