Connect with us

News

Wasu Na Ɗaukar Nauyin Ta’addanci Domin Cim Ma Muradun Siyasa  — Ministan Tsaron Nijeriya

Published

on

f240804e66d0d7c85ef90ead250d5c4c0efbcf924d6b7b19df6a6e121df5ac6a MAIN

Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa, ya zargi wasu daga cikin ‘yan ƙasar da hannu wajen haddasa rikice-rikicen tsaro domin cim ma muradun siyasa, yana mai cewa tashin hankali na ƙaruwa musamman a lokutan da ake tunkarar zaɓe.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da TRT Afrika Hausa yayin halartar Antalya Diplomacy Forum da aka gudanar a ƙasar Turkiyya.

Advertisement

Dakarun Sojin Najeriya  Guda 200 Zasu Samu Horo A Turkiyya

Ya ce abin takaici ne yadda ake samun ƙarin hare-hare a lokutan zaɓe, yana mai jaddada cewa akwai waɗanda ba sa fatan zaman lafiya a ƙasar.

Advertisement

“Akwai waɗanda ba sa son zaman lafiya, kuma duk lokacin da zaɓe ya zo sai ka ga rikici ya ƙaru,” in ji shi.

Ministan ya gargadi masu neman shugabanci da su guji amfani da tashin hankali wajen cim ma burinsu, yana mai cewa kashe-kashe ba zai amfani kowa ba.

Advertisement

“Idan kana son zama shugaba, ba dole sai ka tura mutane su kashe wasu ba,” ya ƙara da jaddadawa.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa kai da jami’an tsaro wajen yaƙi da masu haddasa rikici, yana mai cewa wasu daga cikinsu ba sa ƙaunar ƙasar, yayin da wasu ƙasashen waje ke cin gajiyar halin da ake ciki.

Advertisement

Ministan ya ce haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, yana mai cewa zaman lafiya ne ginshiƙin cigaba.

A cewarsa, jami’an tsaro na ci gaba da aiki tukuru dare da rana domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar, tare da nuna fatan samun nasara da taimakon Allah.

Advertisement

 

Tasirin rikice-rikicen duniya

Advertisement

Dangane da halin rashin tabbas da ake fama da shi a duniya, Ministan ya bayyana cewa rikice-rikicen ƙasa da ƙasa na da tasiri kai tsaye ga Nijeriya.

Ya ambaci tashin hankali a ƙasashe kamar Iran, Isra’ila da Amurka, da kuma rikicin Rasha da Ukraine, yana mai cewa suna tasiri ga tattalin arziki da tsaro a duniya baki ɗaya.

Advertisement

Ya ƙara da cewa hauhawar farashin kayayyaki da man fetur da ake gani a yanzu na da alaƙa da waɗannan rikice-rikice.

Ministan ya kuma bayyana cewa halartar mutane kusan 5,000 a taron diflomasiyyar na Antalya na nuna yadda ƙasashe ke nuna damuwa kan halin da duniya ke ciki.

Advertisement

A ƙarshe, ya jaddada cewa matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta ba ita kaɗai ba ne, yana mai kira ga ƙarin haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma domin shawo kan matsalolin.

>“Idan babu zaman lafiya, ba za a samu cigaba ba,” in ji shi, yana mai jaddada muhimmancin tattaunawa da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe wajen samar da mafita mai ɗorewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending